Lafiya Jari Ce
Abubuwan da ya kamata a sani kan sabuwar cutar Hantavirus da ta ɓulla
- Autor: Vários
- Narrador: Vários
- Editora: Podcast
- Duração: 0:10:06
- Mais informações
Informações:
Sinopse
Shirin Lafiya Jari Ce a wannan makon ya yi nazari kan cutar Hantavirus da duniya ta ga ɓullarta a baya-bayan nan, lamarin da ya sanya fargaba a zuƙatan jama’a, musamman ganin yadda ake alaƙanta wannan cuta a sahun masu haɗari da tarihi ya nuna yaddda suka yiwa duniya ɓarna matuƙa. Cikin watan jiya ne aka ga ɓullar wannan cuta a wani jirgi da ya taso daga Argentina zuwa Cape Verde, sai dai tilas ya samu izinin yada zango a tsibirin Spain sakamakon yadda cutar ta kashe mutane 3 ta kuma harbu wasu mutum 8. Duk da cewa Majalisar ɗinkin duniya ta nesanta alaƙar wannan cuta ta Hantavirus da kasancewa covid-19 ta biyu amma mutane na cike da fargaba. Ku latsa alamar sauti don sauraron ciakken shirin tare Azima Bashir Aminu........