Informações:
Sinopse
Shirin Lafiya yana tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jamaa, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Talata da yamma.
Episódios
-
Kamaru ta yi nasarar rage mutuwar mata yayin haihuwa a cikin shekaru 4
01/12/2025 Duração: 10minA wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan wasu alƙaluma da ke nuna cewa cikin shekaru 4 da suka gabata Kamaru ta yi nasarar rage yawan matan da ke mutuwa a lokacin haihuwa ko kuma goyon ciki. Alƙaluman hukumar kula da lafiyar yara da na DHS mai tattara alƙaluman jama’a sun nuna da cewa da kusan rabi ne aka samu raguwar mace-macen matan, inda daga mace-macen mata dubu 2 cikin dubu 100 a 2018 adadin a yanzu ya dawo mace-macen mata 406 cikin dubu 100 duk shekara wanda ke nufin gagarumar nasara, kodayake ministan lafiya na ƙasar Manaouda Malachie ya ce sun yi amfani da wasu tsare-tsare gabanin samun wannan nasara.
-
Fahimtar ƙwararru game da tasirin Hamma ga lafiyar ɗan adam
24/11/2025 Duração: 09minShirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir a wannan makon ya mayar da hankali kan wasu daga cikin ɗabi’un jikin ɗan adam da kan faru ba tare da shiri ba, cikin waɗannan ɗabi’u kuwa har da hamma, inda shirin zai duba tasirinta ga lafiyar ɗan adam. Rubuce-rubucen masana game da ɗabi’ar ta hamma na alaƙanta ta da barci ko gajiya ko kuma yunwa, sai dai fa masanan sun kuma bayyana cewa Hammar na taka muhimmiyar rawa a tsarin lumfashin ɗan adam, musamman ta fuskar daidaita yawan iskar da mutum ke shaƙa wato Oxygen da kuma wadda ya ke fitarwa wato Carbon dioxide. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
-
Yadda cutar Suga ke mamaya a ƙasashen Afrika
17/11/2025 Duração: 10minShirin lafiya jari ce na wannan mao ya mayar da hankali ne kan wani rahoto da ke cewa mutane akalla miliyan 24 ne ke fama da cutar Suga a Nahiyar Afrika kawai. Wannan kuwa na faruwa ne a dai-dai lokacin da cutar ke sauya salo da tsanani ga masu fama da ita, baya ga bijirewa magani. Danna alamar sauraro domin jin cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu.
-
Mutane fiye da dubu 28 na mutuwa duk shekara saboda gurɓacewar iska a Ghana
10/11/2025 Duração: 10minA wannan makon shirin Lafiya jari ce ya mayar da hankali kan wani bincike a Ghana da ke nuna yadda mutane sama da dubu 28 ke mutuwa duk shekara saboda gurbacewar iska. Alƙaluman hukumar kula da Lafiya ta Ghana ne ke sanar da wannan adadi, wanda kai tsaye ke nufin duk mintuna 19 wannan matsala ta gurɓatacciyar iska kan sabbaba mutuwar mutum guda a wannan ƙasa ta yammacin Afrika, batun da ke buƙatar kulawar gaggawa don ɗaukar matakan da suka dace. Latsa alamar sauti don sauraren shirin tare da Azima Bashir Aminu...